Daren 1 ga Watan Rajab
Sallar Daren 2 ga Watan Rajab
An karbo daga Manzon Allah (saww) cewa: Duk wanda yayi a daren biyu ga watan Rajab, salla Raka’a 10 (5x2), ya karanta a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya. Suratul Kafiroon sau daya.
Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa, babba ko karami, kuma ya rubuta sunansa a cikin musalleen har zuwa shekara mai zuwa.
Sallar Daren 3 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (saww) cewa: “Duk wanda yayi a daren uku ga watan Rajab, sallah raka’a 10 (5x2), ya karanta a kowace Raka’a Fatiha sau Daya (x1) da kuma Suratul Nasr sau 5 (x5).
Allah zai gina masa gida a Aljannah, tsawonsa da fadinsa zai ninka girman duniya sau 7.
Sai kuma Sallar da akeyi a wayewar gari, wato Ranar 3 ga watan Rajab
Sallah Ranar 3 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a ranar uku ga watan Rajab, sallah Raka’a 4 (2x2), yana karantawa a kowace Raka’a bayan Suratul Fatiha aya ta 163 zuwa 165 dake cikin Suratul Baqarah (S. Baqarah 163-165).
Allah zai ba shi ladan da ba za a iya siffanta ta ba.
Sallar Daren 4 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallam) cewa: “Duk wanda yayi a daren hudu ga Watan Rajab, Sallah Raka’a 100 (50x2) yana karantawa a kowace Raka’ar farko Suratul Fatiha da kuma Suratul Falaq. Sannan a kowace Raka'a ta biyu kuma bayan Suratul Fatiha sai ya karanta suratul Naas.
Mala'ika zaya sauko daga kowace sama domin ya rubuta masa lada har zuwa ranar kiyama, a lokacin da fuskarsa zatayi haske kamar wata, kuma a bashi littafinsa na ayyukansa a hannun dama, kuma zai amfana da hisabi mai sauki.
Sallar Daren 5 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W. W) cewa: “Duk wanda yayi a daran biyar ga watan Rajab, salla Raka’a 6 (3x2), yana karantawa a kowace Raka’a Suratul Fatiha sau daya (x1), sai kuma Suratul Ikhlaas sau Ashirin da Biyar (x25). Allah zai ba shi ladan Annabawa 40, masu gaskiya 40, shahidai 40, kuma zai sa shi ya wuce kan siradi kamar walƙiya, kamar yana kan dokin haske.
Allah ya karbi Ibadun mu.
