Furucin Sheikh Zakzaky daya Hana Kafircin Duniya Bacci

Zakzaky
Sheikh Ibrahim Yaqub Al-Zakzaky 



-Sheikh Ibrahim Yaqub Al-Zakzaky 

Nayi Tawaye ma tsarin dake tafi da ita wannan qasa wanda ya fanɗarema na Allah, kuma nayi wa shuwagabanninta tawaye kuma ban yadda da shugabancin suba, ban kuma yadda da ainihin tsarin da suke aiki dashi ba.


A madadin wannan don kuma kowa yayi mani shaida na daɗa jaddada imani na ga Allah Ta'ala shi kaɗai da kuma Manzon sa Muhammad (S) da kuma Alqur'anin daya aiko Manzonsa dashi da kuma shari'ar dake ciki.


Jagora yayi wannan furucin ne a Funtua Declaration.


Ɗan tsokaci 


Idan kukayi duba akan wannan furucin dasu Jagora Sayyid Zakzaky sukayi zakuga cewa sun fassara Kalmar shahada ne.


Inda jagora ya kore kowa sannan ya tabbatar da Allah.


Kuma wannan shine aikin da Manzon mu Muhammad (S) yayi kuma shine dukkan annabawa sukayi, to shima Sayyid Zakzaky hanyar suce yabi.


Kuma wannan itace hanyar Allah guda ɗaya tilo, duk wanda ya nufaci Allah to dole sai ya bita.


Fatan mu Allah yasa damu za'ayi Allah kuma ya qarawa Jagora Sayyid Zakzaky Lafiya da mai Dakin sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post