Sallar Daren Shida na Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk wanda yayi a daren shida ga watan Rajab, sallah Raka’a 2, yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya sai kuma Ayat al-Kursiy sau bakwai (x7).
Wani mai kira daga sama zai kira, yace “Ya bawan Allah! Lalle ne kai majibincin Allah ne. Duk harafin daka karanta a cikin wannan sallar akwai ceto daga musulmi, kana da ayyuka na alheri dubu saba’in, kuma kowanne daga cikin ayyukan alheri a wajen Allah ya fi duwatsun duniya girma”.
Sallar Daren 7 ga Watan Rajab
Manzon Allah (s.a.w.w) yace idan mutum yayi Sallah Raka'a 4 a daren 7 ga Watan Rajab, yana karantawa a kowace raka'a bayan suratul Hamd sai ya karanta suratul Tauhidi sau uku (x3), Suratul Falaq sau daya (x1), Suratul Naas sau daya (x1). Bayan ya gama Sallar sai yayi Salatin Annabi sau Goma (x10) da kuma Tasbeehate Arba' Sau Goma (x10).
Allah zai ba shi masauki a karkashin Al-Arsh, kuma ya bashi ladan mai Azumi a watan ramdhan. Sannan kuma Har ya idar da sallar Mala'iku suna yi masa Addu'ar gafara. Allah zai sauwake masa radadin mutuwa kuma ya tseratar dashi daga matsi a cikin kabari. Ba zai mutu ba har sai yaga Masaukin sa a Aljanna, kuma sannan zaya tsira daga wahalhalun qiyama.
Sallar Daren 8 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren takwas ga watan Rajab, sallah Raka’a 20 (10x2), a kowace raka’a bayan Suratul Fatiha, yana karanta wadannan Surori kowace sau 3 Suratul Tauhidi, suratul Kafiroon da kuma suratul Falaq.
Allah zai bashi ladan masu godiya da ladan mutane masu dauriya kuma ya daukaka sunansa a cikin masu gaskiya kuma duk harafin da ya karanta, Allah zai bashi ladan masu gaskiya da shahidai baki daya. sannan kuma zai zama Kamar ya karanta Alqur'ani ne a cikin watan Ramadan. Mala'iku saba'in ne za su yi masa maraba da zarar ya fito kabari. Wadannan Mala'iku za su yi masa albishir da Aljanna kuma su yi masa jagora zuwa gare ta.
Sallar Daren Tara 9 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: Duk wanda yayi sallah Raka’a 2 a daren tara ga watan Rajab, wanda a kowace raka’a ya karanta Suratul Fatiha sau daya, sai kuma Suratul Takathur sau biyar (x5).
Allah (T) ya gafarta masa, ya ba shi ladan hajji da umra dari, ya saukar masa da nau'i na rahamah guda miliyan, ya tsare shi daga wuta kafin ya tashi daga wurin da yake. Idan ya mutu a cikin kwanaki tamanin, za a dauke shi a matsayin shahidi.
Sallar Daren 10 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (saww) cewa: “Duk wanda yayi a daren goma ga watan Rajab, sallah raka’a 12 (6x2), a kowace raka’a yana karanta suratul Fatiha sau Daya (x1), sai kuma Suratul Ikhlaas sau uku (x3).
Allah (T) zai gina masa Fada akan wani ginshiki da aka yi da jajayen yakutu... A ciki akwai dakuna dari bakwai wanda kowanne ya fi wannan duniya girma. Duk dakunan da ke ciki an yi su ne da zinariya, da azurfa, da yakutu da Duwatsu masu Daraja. Sannan kuma Akwai gidaje da yawa acikin wannan fadar kamar yadda taurari suke a sararin samaniya kuma aciki akwai abubuwan da mutum ba zai iya kwatanta su ba.
Allah (T) ya karbi Ibadun mu.
