Sallolin Daren 11,12,13,14 da kuma 15 ga Watan rajab


 


Sallar Daren 11 ga Watan Rajab


 An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha daya (11) ga watan Rajab, sallah Raka’a 12 (6x2), wanda a kowace raka’a yake karanta suratul Fatiha sau daya (x1), sai kuma Ayatul Kursiyyu sau goma sha biyu (x12). 

Allah zai bashi ladan wanda ya karanta Attaura, Injila, da zabura, da kuma Alqur'ani, dama duk wani littafi da Allah –Madaukakin Sarki ya saukar ga Annabawansa. Sannan kuma Wani mai kira daga Al'arshi zai yi kira, "Ku sake ayyukanku domin haqiqa Allah Ya gafarta muku."


Sallar Daren 12 ga Watan Rajab


 An Ruwaito daga Manzon Allah (saww) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha biyu ga watan Rajab, sallah Raka’a 2, ya karanta a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1) sai kuma Wadannan ayoyin dake cikin Suratul Baqara 285-286 sau goma (x10).

 Allah zaya bashi ladan masu umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, da ladan 'yanta bayi saba'in daga zuriyar Annabi Isma'il (AS), kuma Allah zaya yi masa rahama saba'in.


Sallar Daren 13 ga Watan Rajab


 An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha uku ga watan Rajab, sallah raka’a 10 (5x2), wanda ya karanta a raka’ar farko suratul Fatiha sau daya da Suratul Adiyaat sau daya (x1), sai kuma a sauran raka'o'in tara (9) yana karantawa a cikin su suratul Fatiha da Suratul takathur sau daya (x1).

Allah zai gafarta masa koda iyayensa sun tsine masa, Munkar ko Nakir ba zasu kusance shi ba balle su tsorata shi, kuma zai tsallake Siradi kamar walkiya kuma za'a mika mashi littafinsa na aikinsa a hannun damansa, sannan kuma a nauyaya littafin na ayyukansa, sannan kuma za'a bashi garuruwa dubu a Aljanna.


Sallar Daren 14 ga Watan Rajab


 An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha hudu ga watan Rajab, sallah Raka’a 30 (15x2), yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha, suratutul Ikhlaas, sai kuma Aya ta 110 cikin suratul Kahf dukkanin su sau daya.

Na rantse da wanda yake juya rayuwata, zai gama sallarsa tsarkakakke ko da kuwa zunubansa sun fi taurarin sama, kuma zai kasance kamar ya karanta dukkan littattafan da Allah Ya saukar.


Daren 15 ga Watan Rajab



Post a Comment

Previous Post Next Post