Sallar Daren 16 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk yayi a daren sha shida ga watan Rajab, sallah Raka’a 30 (15x2), yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha sau Daya (x1) sai kuma Suratul Ikhlaas Sau goma (x10).
Allah zai bashi ladan shahidai saba'in kafin ya idar da sallarsa, ranar qiyama kuma haskensa zaya haskaka, kuma zaya yi kama da sararin da ke tsakanin Makka da Madina, kuma Allah zaya bashi kariya daga wuta, da kariya daga munafunci, kuma ya 'yantar dashi daga Azabar kabari.
Sallar Daren 17 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallam) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha bakwai ga watan Rajab, sallah Raka’a 30 (15x2), yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1) da kuma Suratul Ikhlaas sau goma (x10).
Allah zai bashi ladan shahidai saba'in kafin ya gama sallarsa.
Sallar Daren 18 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren sha takwas ga watan Rajab, sallah Raka’a 2, ya karanta a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1), sai kuma suratul Ikhlaas, suratul Falaq da Suratun Naas kowacce sau Goma (x10).
Bayan ya idar da sallarsa Allah zaya gayawa Mala'iku, na gafarta masa zunubansa, saboda wannan Sallar da yayi, koda kuwa zunubansa sun fi na dan kasuwa mai ha'inci. Kuma Allah zaya sanya ramuka shida tsakaninsa da wuta tazarar da ke tsakanin kowane rami ya kai kamar tazarar da ke tsakanin sama da kasa.
Sallar Daren 19 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: Duk wanda yayi a daren sha tara ga watan Rajab, sallah Raka’a 4 (2x2), yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1), Ayatul Kursiyyu sau sha biyar (x15), da kuma “La ilaha illallah” sau sha biyar (x15).
Allah zaya bashi lada kwatankwacin abin da yaba Musa (As). Sannan Ga kowace harafi,
za’a bashi ladan shahidi. Allah zai tashe shi da Mala'iku masu yi masa bushara guda uku. Na farko ba zai fuskanci matsala ba a wurin tsayawa a lahira, na biyu kuma ba za’a yi masa hisabi ba, na uku kuma zaya shiga Aljanna ba tare da hisabi ba.
Kuma da zarar ya tsaya a gaban Allah, Allah Madaukakin Sarki zaya yi masa sallama ya ce masa, ya bawana! Kada kaji tsoro ko bak'in ciki tunda na yarda da kai kuma Aljannah ta halatta agareka.
Sallar Daren 20 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren ashirin ga watan Rajab, sallah Raka’a 2, ya karanta a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1) da suratul Kadri sau biyar (x5).
Za’a bashi ladan Ibrahim da Musa da Yahaya da Isa (As) daga wurin Allah. Duk wanda ya yi wannan sallar Aljanu ko Mutane baza su cutar dashi ba. Kuma Allah zai dube shi da rahama.
