Sallolin Daren 21,22,23,24 da kuma 25 ga Watan Rajab




 Sallar Daren 21 ga Watan Rajab


An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da daya ga watan Rajab, sallah Raka’a 6 (3x2), yana karantawa a kowace raka’a, Suratul Fatiha sau daya (x1), suratul kauthar sau goma (x10), suratul Ikhlaas sau goma (x10).

Allah zai umurci Mala'iku - Marubuta masu girma (Kiraman Katibin) kada su rubuta masa wani munanan ayyuka har tsawon shekara guda, su rubuta masa kyawawan ayyukansa. Na rantse da wanda ya sanya ni Annabci cewa duk wanda ya so ni kuma yana son Allah kuma ya yi wannan sallar, idan kuma bai iya tashi sai yayi sallar a zaune – Allah zaya yi alfahari da ita a wajen Mala’ikunSa, ya ce: “Lallai ni na gafarta mashi.

Sallar Daren 22 ga Watan Rajab



An Ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallam) cewa: Kuyi sallah Raka’a 8 (4x2), a kowace raka’a ku karanta Suratul Fatiha sau daya (x1), da kuma Suratul Kafiroon sau bakwai (x7). Bayan kun idar da sallar sai kuyi salati ga Annabi da alayensa (saww) sau goma (x10) kuma ku nemi gafara (astaghfirullah Rabbi wa atooboIlayh) sau goma (x10).

Lada (wanda yayi) Ba zai fita daga duniya ba har sai ya ga matsayinsa a Aljanna. (kuma) zaya mutu yana musulmi kuma zaya sami ladan Annabawa saba'in.


Sallar Daren 22 ga Watan Rajab daga “Manazeral Akherah na Shaikh Abbas Qummi”

Za’ayi sallah Raka'a 8 (raka'a 4X2) a kowace Raka'a bayan Suratul Fatiha, sai a karanta Suratul Tauhidi sau bakwai (x7). Bayan kammala sallar sai ayi salatin Annabi sau Goma (x10), sannan ayi Istigfari “Astaghfirullah Rabbi wa atooboIlayh” sau Goma (x10). An ruwaito cewa tana da amfani sosai lokacin Mutuwa.


Sallar Daren 23 ga watan Rajab



An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da uku ga watan Rajab, sallah Raka’a 2, yana karantawa a kowace raka’a suratul Fatiha sau daya (x1) da Suratul Dhuha sau biyar (x5).

Allah zaya bashi Matsayi a gidan Aljannah akan kowane harafi daya karanta, kuma zaya samu Matsayi a Gidan Aljanna ga duk wanda bai yarda da Allah ba namiji ko mace, kuma Allah zai ba shi ladan hajji saba'in, da ladan halartar Jana'iza Dubu daya (1000), da ladan ziyarar marassa lafiya dubu daya (1000), da ladan biyan bukatun musulmi Dubu daya (1000).

Sallar Daren 24 ga Watan Rajab


An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk wanda yayi a Daren Ashirin da hudu ga watan Rajab, sallah Raka’a 40 (20x2), yana karantawa a kowace Raka’a. Suratul Fatiha sau daya (x1), Aya ta 285 da ta 286 dake cikin Suratul Baqarah sau daya (x1), sai kuma Suratul Ikhlaas sau daya (x1).

Allah zai rubuta masa Ladan ayyukan alheri dubu, ya shafe zunubansa Dubu, ya daukaka darajarsa darajoji dubu. Kuma ya saukar da mala'iku dubu daga sama suna masu daga hannayensu suna yi masa salati. Allah –Maxaukakin Sarki zai ba shi lafiya a duniya da Lahira kuma ya kasance kamar ya riski lailatul kadari.



Sallar Daren 25 ga Watan Rajab



An Ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa alihi Wasallam) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da biyar ga watan Rajab, sallah Raka’a 20 (10x2) tsakanin Magriba da Isha’i. Yana karantawa a kowace raka'a Suratul Fatiha sau daya (x1), aya ta 285 da ta 286 dake cikin Suratul Baqarah sau daya (x1), da kuma suratul Ikhlaas sau daya (x1).

Allah zai kareshi da Matarsa da Addininsa da Dukiyarsa da Rayuwarsa da Lahirarsa kuma za’a gafarta masa kafin ya tashi daga wurinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post