Sallar Daren 26 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da shida ga watan Rajab, sallah Raka’a 12 (6x2), yana karantawa a kowace raka’a, Suratul Fatiha sau daya (x1), da kuma suratul Ikhlaas sau arba'in (x40) (A wasu Ruwayoyin ance sau hudu).
Mala'iku zasu rungume shi kuma duk wanda Mala'iku suka rungume, zaya tsira daga tsayarwa akan Siradi da Hisabi da Ma'auni. Kuma Allah zaya nada Mala'iku saba'in domin su nemi gafarar Allah Agareshi, su rubuta masa lada, da bayyana girman Allah a gare shi, su ce: "Ya Allah! Ka gafarta wa wannan bawa mai bauta!" har zuwa safe.
Daren 27 ga Watan Rajab
Sallar Daren 28 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (SAWW) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da takwas ga watan Rajab, sallah Raka’a 12 (6x2), yana karantawa a kowace raka’a. Suratul Fatiha sau daya da Suratul A'alaa da suratun Qadr sau goma kowanne, bayan an idar da sallah sai ayi salati da Istigfari sau 100 kowanne.
Allah Ta'ala zai rubuta ladan bautar da Mala'iku suka yi gareshi.
Sallar Daren 29 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (S.A.W.W) cewa: “Duk wanda yayi a daren Ashirin da tara ga watan Rajab, sallah Raka’a 12 (6x2), yana karantawa kowace raka’a Suratul Fatiha sau daya (x1) da Suratul A'alaa da suratun Qadr sau goma kowanne, bayan an Idar da sallar sai ayi salati da Istigfari sau 100 kowanne.
Allah Ta'ala zai rubuta Mashi Ladan bautar da Mala'iku suka yi Gareshi.
Sallar Daren 30 ga Watan Rajab
An Ruwaito daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallam) cewa: “Duk wanda yayi a daren talatin ga watan Rajab, sallah Raka’a 10 (5x2), yana karantawa a kowace Raka’a suratul Fatiha sau daya (x1) da kuma Suratul Iklaas sau goma (x10).
Allah zaya bashi Garuruwa Bakwai a cikin Aljanna kuma za’a fitar da shi daga cikin kabari fuskarsa tana haskakawa kamar cikakken wata. Zai haye Siradi kamar walƙiya kuma zaya tsira daga wuta.
