Mai bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara kan batun azabtarwa, Alice Jill Edwards, ta bayyana cewa akwai bukatar bincike kan cin zarafin bil'adama da sojojin Isra'ila suka aikata yayin yakin kashe-kashe da lalata da aka yi a yankin Gaza da ke karkashin killace.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Edwards ta jaddada muhimmancin yarjejeniyar tsagaita wuta bayan watanni 15 na luguden wuta da korar mutane daga gidajensu a Gaza, da kuma mummunan tasirin da aka fuskanta tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Ta ce dawowar Falasɗinawa “babban ci gaba ne,” tana mai nuna fatan samun zaman lafiya mai dorewa da adalci bayan wahalhalun da aka sha.
Ta ambaci kisan gillar da gwamnatin Isra'ila da masu mara mata baya suka yi a kananan yankunan Gaza, wanda ya salwantar da rayukan akalla mutane 47,000, galibinsu mata da yara.
Edwards ta yi kira da a aiwatar da tsagaita wutar yadda ya kamata domin zama wata hanya ta samun zaman lafiya mai dorewa. “Wannan rana ce da mutane da dama suka yi fatan ganin ta.”
Wadannan kalamai sun zo ne bayan fara aiwatar da matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Isra’ila da Hamas.
Edwards ta kuma nuna damuwa kan halin da dubban 'yan Falasdinawa da aka kama ke ciki a gidajen yarin Isra’ila da zarge-zargen da aka yi musu.
“Dole ne a gudanar da cikakken bincike kan duk wani zargi, a gurfanar da masu laifi, sannan a bai wa dukkan wadanda aka azabtar da adalci da tallafin murmurewa.”
Wasu daga cikin fursunonin Falasdinawa suna fuskantar azabtarwa, yunwa, rashin samun kulawar lafiya da ta dace, da kuma katse alaka da duniya baki daya, har da iyalansu.
A wani bangare na jawabanta, Edwards ta yi kira ga gwamnatin Isra'ila da ta bai wa Kwamitin Kula da Sha'anin Jin Kai na Red Cross damar samun cikakken bayani kan dukkan Falasdinawa da ke tsare a gidajen yari ba tare da bata lokaci ba.
