Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Iran zai ci gaba da bunkasa a shekara mai zuwa.
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya fitar ranar Litinin ya nuna cewa IMF ta yi hasashen tattalin arzikin Iran zai karu da kashi 3.1% a 2025, wanda ya yi kasa da matsakaicin ci gaban yankin na kashi 3.9%.
IMF ta kuma yi hasashen cewa jimillar arzikin Iran (GDP) zai karu da dala biliyan 29 zuwa dala biliyan 463 a shekara mai zuwa.
An kuma yi hasashen cewa bangaren tattalin arzikin da ba na man fetur ba na Iran zai karu da kashi 2.3% a 2025.
IMF ta kiyasta cewa Iran za ta samar da matsakaicin ganga miliyan 3.1 na mai a kullum a shekara mai zuwa, yayin da samar da iskar gas zai kai daidai da ganga miliyan 5.2 na mai a kullum, lamarin da zai sa Iran ta zama ta biyu a yankin wajen samar da makamashin hydrocarbons bayan Saudiyya.
IMF ta ce fitar da mai daga Iran za ta kai matsakaicin ganga miliyan 1.6 a kullum, yayin da fitar da iskar gas za ta kai daidai da ganga miliyan 0.4 a kullum a shekarar 2025.
IMF ta hasashen cewa hauhawar farashin kaya a Iran za ta ci gaba da raguwa zuwa kashi 29.5% a badi, mafi karanci cikin shekaru hudu, amma har yanzu tana da yawa fiye da sauran kasashen yankin Gabas ta Yamma.
Asusun ya kuma yi hasashen cewa Iran za ta ci gaba da samun ribar asusun hada-hadarta na kasashen waje a 2025 har zuwa dala biliyan 13.9, wanda ya fi na yawancin kasashen yankin.
Bayanai daga IMF sun nuna cewa kadarorin waje da Iran za ta iya amfani da su za su kai dala biliyan 33.8 a shekara mai zuwa duk da ci gaba da takunkumin Amurka da ke hana kasar samun damar yin amfani da ayyukan banki.
Har ila yau, Iran za ta ci gaba da rike kaso mafi karanci na basussukan waje ga GDP, wanda zai tsaya a kashi 1.8% a 2025, mafi karanci a duk fadin yankin.