An samo gawarwakin mutane 97 a Rafah yayin da ake ci gaba da neman mutane 10,000 da aka rasa a Gaza

 


Majiyoyin lafiya sun bayyana cewa an samo gawarwakin sama da mutane 97 a Rafah, bayan fara yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta bayyana a ranar Litinin cewa Falasdinawa 60 ne suka mutu a ranar farko bayan fara tsagaita wutar.

Hukumar lafiya ta Falasdinu na tsammanin cewa gawarwakin da ba a samo ba zasu kai kimanin mutane 10,000, wasu na kuma ikirarin cewa adadin zai iya kaiwa 15,000.

Hakanan an ce gawarwakin kusan 2,840 sun ɓace ta tururi "ba tare da alama ba" saboda yanayin zafin jiki mai tsanani da haramtattun makaman Isra’ila suka haifar.

Hare haren Bama bamai na Isra’ila a Gaza ya haifar da lalacewar ko rushewar fiye da kashi biyu bisa uku na dukkan gine-ginen yankin.

Samo gawarwakin mutanen da suka mutu ya kuma kara wahala tun da sojojin Isra’ila ke kai hare-hare akai-akai kan rundunonin tsaron fararen hula.

A cikin yakin kisan kiyashi na Isra’ila a Gaza, membobin tsaron fararen hula 99 ne suka mutu, yayin da 319 suka jikkata. Akalla, membobin tsaron fararen hula na Gaza 27 ne aka sace su daga hannun sojojin Isra’ila, kuma har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu, tun daga ranar Litinin, adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya zarce 47,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post