Hezbollah ta yi murnar "babbar nasarar" Falasdinawa a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta

 


Hezbollah ta taya al’ummar Falasdinu murna bisa “babbar nasarar” da aka samu a cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, kungiyar gwagwarmayar ta Lebanon ta bayyana cewa wannan nasara makura ce "ta jajircewa wadda ta zama alama ta tarihi" bayan fiye da watanni 15 na mummunan hare haren kisan kiyashi daga Isra’ila.

Ta kuma ce wannan nasara "misali ce da ya kamata a bi wajen fuskantar hare-haren Sahayoniya da na Amurka a kan al’ummarmu da yankinmu."

“Kasar Amurka tana da cikakken hadin kai a cikin laifuka da kisan kiyashi da abokan gaba suka aikata a kan al’ummar Falasdinu.”

Hezbollah ta kara da cewa, "Amurka tana da cikakken alhakin wannan saboda goyon bayan da take bayarwa ga wannan mamayar ta fuska daban-daban—soja, tsaro, leken asiri, siyasa, da diplomasiyya."

"Yarjejeniyar tsagaita wutar ta zama wani sabon tsari wanda ke nuni da cikas ga abokan gaba na Sahayoniya da masu goyon bayansu, kuma tana mai tabbatar da cewa lokacin yi wa wasu shugabanci ba tare da la'akari da ra'ayin jama'a ba ya wuce, kuma 'yancin al'umma na da karfi fiye da dukkan na'urorin yaki na ta'addanci na Sahayoniya da Amurka."

Yarjejeniyar ta zama wata nasara ta siyasa da aka haɗa da wata nasara ta soja, wanda ke nuna cewa Isra’ila ba ta samu nasarar cimma burinta na yaki ba.

Hezbollah ta bayyana cewa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar sanya sharuddan gwagwarmaya ba tare da janyewa daga hakkin al’ummar Falasdinu ba, yana nuni da nasara ta siyasa da aka haɗa da nasarar soja.

Ta ce gwagwarmayar Falasdinu ta nuna karfinta da ikon ta gurin karya girman kai da zaluncin abokan gaba a cikin wannan yakin.

"Ta tabbatar da cewa wannan karamar kasar ta wucin gadi mai rauni wadda ba zata iya tsayuwa ko ci gaba ba, ba zata ji daɗin tsaro ko zaman lafiya ba matuƙar ta ci gaba da kutse a kan al’umma, ƙasar mu, da wuraren ibadar mu."

Hezbollah ta kuma yi tir da shirun al'ummar duniya kan laifukan da Isra’ila ta aikata.

"Abinda mamayar Sahayoniya ta yi a wannan yaki ta hanyar aikata mummunan kisan kiyashi, wanda ya shafi fararen hula, yara, mata da tsofaffi, zai kasance shaida ta tarihi ga tashin hankali na wannan tsarin mulki da masu goyon bayansa."

Ta ci gaba da cewa, "Laifukan Isra’ila za su kasance a zuciyar zukatan al’umma masu zuwa, kuma wani tabo ne a fuskokin al’ummar duniya da suka yi shiru ko rashin kulawa."

A wani bangare na sanarwar, Hezbollah ta gode wa Iran da bangaren gwagwarmaya akan dangantakar ta da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka samu a Gaza.

"Mun taya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gwagwarmayar Musulunci a Iraki murna, tare da ‘yan uwammu a Yemen."

Post a Comment

Previous Post Next Post