Wani sojan ajiyar ko ta kwana (reservist soldier) na Isra’ila ya mutu, yayin da wasu sojoji hudu suka jikkata bayan motarsu ta taka bam a gefen hanya yayin wani samame a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
A cewar jaridar Isra’ila Yedioth Ahronoth, fashewar ta faru a garin Tammun, kimanin kilomita 13 arewa maso gabas da Nablus, a ranar Litinin.
Jaridar ta kara da cewa sojojin suna cikin wata mota mai sulke lokacin da bam din ya tashi.
Dakarun Isra’ila sun bayyana sunan sojan da ya mutu a fashewar, wanda ke da shekaru 31, a matsayin Eviatar Ben Yehuda.
Sun kuma sanar da cewa wani kwamandan bataliya da ke kusa da shi ya samu munanan raunuka, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa.
A baya, wani matashi dan Falasdinu ya rasa ransa, yayin da wasu da dama, ciki har da yara biyu da wani tsoho, suka jikkata yayin da dakarun sojin Isra’ila suka mamaye garin Sebastia da ke kusa.
Kungiyar Red Crescent Society ta Falasdinu (PRCS) ta bayyana cewa an harbe Ahmad Rashid Rushdi Jazar, mai shekaru 14, a kirji da harsasai yayin samamen da aka kai da maraicen Lahadi.
An garzaya da shi asibiti, inda ya mutu daga munanan raunukan harbin bindiga da ya samu.
Shugaban garin Sebastia, Mohammed Azem, ya ce sojojin Isra’ila sun harba harsasai masu rai, bama-bamai masu firgita, da hayaƙi mai guba kan mazauna yankin da gidajensu yayin arangamar. Wasu masu zanga-zanga sun samu matsalar numfashi sakamakon shakar hayaƙin.
A Yammacin Kogin Jordan ta kudu, PRCS ta ce tawagoginta sun kai mutane biyu da suka jikkata asibiti. Daya, wani saurayi mai shekaru 17, ya samu rauni daga harbin bindiga a hannu, yayin da wani yaro mai shekaru 11 ya ji rauni a yayin arangamar a garin Idhna.
Shaidu sun ce samamen sojin Isra’ila a garin ya dauki kimanin sa’o’i biyu kafin dakarun suka janye. Arangama ta barke yayin samamen, inda aka yi amfani da harsasai masu rai, na roba, da hayaƙi mai sa hawaye.
Hakan ya faru ne yayin da daruruwan iyalan fursunonin Falasdinu suka taru a wajen gidan yari na Ofer da ke Yammacin Kogin Jordan, suna jiran sakin mutane 90, yawancinsu mata da yara, a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas.
A cikin ‘yan shekarun nan, sojojin Isra’ila sun gudanar da samame masu yawa a Yammacin Kogin Jordan, wanda ya tsananta bayan fara yakin kisan kiyashi a Gaza ranar 7 ga Oktoba, 2023. Haka zalika, ‘yan sandan yahudawan haramtacciyar mazauna sun kai hare-hare kan Falasdinawa.
A kalla Falasdinawa 859 ne suka mutu, yayin da sama da 6,700 suka jikkata daga harbin sojojin Isra’ila a yankin da aka mamaye, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta tabbatar.
Tags
Isra'ila