Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito a ranar Juma’a cewa adadin mutanen da suka kashe kansu na iya zama fiye da haka.
Dakarun sojojin Isra’ila dai sun ki bayar da adadin su a hukumance, duk da alkawarin da suka yi na yin hakan.
Rahoton ya ce dubban dakarun sun nemi taimakon asibitocin da ke kula da lafiyar kwakwalwa, kuma kusan kashi daya bisa uku na waɗanda abin ya shafa suna fama da alamun cutar tashin hankali ta bayan yaki (PTSD).
Adadin sojojin da ke fama da matsalolin tunani zai iya wuce na waɗanda suka ji raunuka na jiki a wannan yakin, in ji rahoton.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kiyashi kan Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, bayan harin bazata da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai a karkashin sunan Operation Al-Aqsa Storm, don mayar da martani ga shekaru masu yawa na zalunci da kashe-kashe da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa.
A wannan yakin da Isra’ila ke kai wa kan Gaza, ya zuwa yanzu an kashe sama da Falasdinawa 44,000, mafi yawan su mata da yara, sannan an jikkata sama da 104,200. Haka nan, dubban mutane sun bace kuma ana zaton suna karkashin ginin da ya rushe.
Tun bayan kaddamar da wannan yakin, Isra’ila ta ƙara matsa lamba kan Falasdinawa da ke Gabashin Kogin Jordan, inda ta kashe daruruwan mutane tare da kama dubban wasu.
