Pentagon ta tabbatar cewa ta tura tsarin makamin kare sararin samaniya (THAAD) tare da sojojin Amurka zuwa Isra’ila

 


Amurka ta tabbatar da cewa ta aika da tsarin makami mai kare sararin samaniya mai suna (THAAD) tare da sojojin ta, domin taimakawa sojojin Isra’ila bayan da gwamnatin Tel Aviv ta kasa kare kanta daga hare-haren da Iran ke kai mata.


A wata sanarwa da mai magana da yawun Pentagon, Maj. Gen. Pat Ryder, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa Shugaba Joe Biden ya ba da izini ga Ministan Tsaron Amurka, Lloyd Austin, don tura baturin tsarin kariya na THAAD tare da tawagar sojojin Amurka zuwa yankunan da Isra'ila ta mamaye domin kara karfafa kariyar Isra’ila daga hare-haren makamai masu linzami na Iran.


"Da umarnin Shugaban kasa, Ministan Tsaro Austin ya amince da tura baturin THAAD tare da sojojin Amurka da za su sarrafa shi zuwa Isra’ila, domin karfafa tsarin kariyar sararin samaniyar Isra’ila bayan hare-haren Iran masu tsanani kan Isra’ila a ranar 13 ga Afrilu da kuma 1 ga Oktoba," in ji Ryder a cikin sanarwar.


Ya jaddada cewa samar da wannan tsarin kariya da sojojin Amurka ke sarrafawa ga Isra'ilawa ya nuna cikakken goyon bayan Amurka ga gwamnatin Tel Aviv.


"Wannan matakin yana tabbatar da alkawarin da Amurka ta dauka wajen kare Isra’ila da kuma kare Amurkawa da suke zaune a Isra’ila daga duk wani harin makami mai linzami da Iran za ta kai," in ji shi, ya kara da cewa, "Wannan na daga cikin sauye-sauyen da rundunar sojin Amurka ta yi a ‘yan watannin baya, don kare Isra’ila da kuma kare Amurkawa daga hare-haren Iran da kungiyoyin da suka shafi Iran."


Ryder ya kuma bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da Pentagon ke samar da tsarin kariya na THAAD da sojojin Amurka ke sarrafawa ga Isra'ilawa ba.


"Ba wannan ne karo na farko da Amurka ta tura baturin THAAD zuwa wannan yanki ba. A shekarar data wuce, Shugaban kasa ya ba da umarnin tura baturin THAAD zuwa Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da aka kai ranar 7 ga Oktoba, domin kare sojojin Amurka da muradun kasar a yankin. Haka kuma a shekarar 2019, Amurka ta tura baturin THAAD zuwa Isra’ila don horo da kuma gudanar da atisayen tsaro a sararin samaniya," in ji shi.


Ana sa ran sojojin Amurka kusan 100 ne za su kasance tare da wannan baturin domin gudanar da tsarin kariya daga harin makamai masu linzami, in ji wani jami’in tsaron Amurka.


A halin yanzu, Amurka ta bayyana a sarari cewa ba ta son gwamnatin Isra’ila ta kai hari kan Iran, musamman kan tashoshin makamashin nukiliya ko wuraren hakar mai na Jamhuriyar ta Islama.


Rahotanni sun nuna cewa a ranar Laraba, Shugaban Amurka Biden ya umarci Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, cewa duk wani martani da Isra’ila za ta mayar kan Iran ta sama to kada su wuce kima ko tsananta fiye da yadda ya dace.

Post a Comment

Previous Post Next Post