Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci dake kare yankin Iraqi daga ta’addanci sun sanar da sabbin hare-haren ramuwar gayya da suka kai kan wasu manyan wuraren Isra'ila da ke yankunan da ta mamaye, ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuka. Wannan hari martani ne ga ci gaba da hare-haren gwamnatin Tel Aviv a Gaza da Lebanon.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta wallafa a tashar Telegram a safiyar Litinin, ta bayyana cewa ta kai hari kan wani muhimmin wuri a Kwarin Jordan ta amfani da jiragen yaki marasa matuka.
Sun bayyana cewa wannan hari wani mataki ne na ci gaba da ƙin amincewa da mamayar da gwamnatin Isra'ila ke yi, kuma yana a matsayin goyon baya ga al'ummar Falasdinawa da ke Gaza da kuma fararen hula na Lebanon, da martani ga kisan gillar da ake yi wa marasa laifi a yankin Falasdinawa.
Kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-hare da lalata muhimman wuraren da ke cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye.
A baya-bayan nan, wata ƙungiya mai suna Guardians of Blood Brigades, wacce ke ƙarƙashin Islamic Resistance in Iraq, ta dauki alhakin kai harin da aka yi da Jirage marasa matuka kan wasu muhimman wuraren Isra’ila biyu a tashar Haifa da ke arewacin yankunan da Isra’ila ta mamaye.
Mayakan na Iraqi sun kuma yi alkawarin ƙara kaimi wajen kai hare-hare kan wuraren Isra’ila. Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba bara, lokacin da gwamnatin Isra'ila ta fara yakin kisan kare dangi a Zirin Gaza, ƙungiyar Islamic Resistance in Iraq ta yi ta kai hare-hare kan wuraren da ke cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye.
Daga wannan hari zuwa yanzu, an kashe akalla Falasdinawa 42,227, yawancinsu mata da yara, sakamakon farmakin sojojin Isra’ila.
