Ofishin Jakadancin Iran a Beirut Ya Shawarci 'Yan Iran Kan Gujewa Tafiya Lebanon

 


Ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Beirut ya bayar da shawara ga 'yan Iran kan cewa su guji tafiya zuwa Lebanon.


A cikin wata hira da IRNA tayi dashi, Konsulan na Iran, Mohammad Fereidouni, ya bayyana cewa ya kamata 'yan Iran su guji ziyartar Lebanon har sai an sanar da sabon bayani, sakamakon yaki da ke ci gaba a kasar.


Fereidouni ya kara da cewa ofishin jakadancin ya tallafawa wasu 'yan Iran da ke son komawa gida daga Lebanon. Sannan kuma ga wadanda har yanzu suke Lebanon kuma suke son komawa Iran ko suna bukatar hidimomin ofishin jakadanci, za su iya tuntubar ofishin jakadancin Iran a Beirut ko kuma su kira lambar 03996708.

Post a Comment

Previous Post Next Post