An Gwabza Kazamin Fada A Yankunan Arewa Da Aka Mamaye

 


Dakarun Redwan, mayaka na musamman na kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kasar Labanon, a wani mataki na bazata, sun shiga matsugunan sahyoniyawan Qiryat Shemona, inda suka gwabza da dakarun gwamnatin, Kamfanin dillancin labaran Samaa na Falasdinu ne ya ruwaito hakan da yammacin jiya Juma'a.


Kafofin yada labaran kasar sun ce an kama wasu sojojin yahudawan sahyoniya, wasu kuma an kashe su ko kuma sun jikkata.


Tashar Channel 12 ta Isra'ila ta sanar da kai wani gagarumin hari da kungiyar Hizbullah ta kai kan yankin Galili da ke arewacin Palasdinu da ta mamaye.


Harin na Hizbullah ya girgiza sojojin Isra'ila, inji tashar.


Kafin haka dai kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayar da rahoton faruwar wani mummunan lamari na tsaro a yankin arewacin Palastinu da aka mamaye.


Jirage masu saukar ungulu na gwamnatin Isra'ila sun kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Haifa.


Tun Bayan da Isra'ila ta kashe shugaban kungiyar Hizbullah Shaheed Sayyed Hassan Nasrallah mako guda da ya gabata, rikici ya kara kamari tsakanin gwamnatin sahyoniyawa da mayakan gwagwarmayar na Islama.

Post a Comment

Previous Post Next Post