Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ta kai hari kan wasu wurare a Palastinu da aka mamaye, kamar yadda kamfanin Dillancin labaran IRNA ya ruwaito daga Aljazeera ayau Juma'a.
Rahoton ya cigaba da cewa an kai harin ne a wasu gurare guda uku.
A baya dai kungiyar gwagwarmayar ta Islama ta kasar Iraki ta sanar da kai hari a wani wuri a yankunan kudancin kasar da wani jirgin sama mara matuki na musamman a karon farko.
A baya dai kungiyar ta gargadi gwamnatin sahyoniyawan da cewa idan har ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, to za ta kara kaimi wajen yakar wannan gwamnati.
