Mayakan Hezbollah Sun Tilastawa Sojojin Isra'ila Ja Da Baya Daga Kan Iyakar Lebanon

 


Hezbollah ta ce mayakan gwagwarmayar Lebanon sun dakile wani yunkurin kutsawa da sojojin Isra'ila suka yi a wasu yankunan kan iyaka da ke kudancin kasar.


Hezbollah ta fada ayau Laraba cewa mayakanta sun yi arangama da dakarun sojin ƙasa na gwamnatin inda suka tilasta musu ja da baya daga garin Odaisseh.


Mayakan kuma sun fafata da sojojin Isra'ila "wadanda suka kutsa cikin kauyen Maroun al-Ras," in ji Hezbollah.


A wata sanarwa da ta fitar a baya, Hezbollah ta ce ta tilastawa sojojin Isra'ila janyewa bayan da suka yi yunkurin kutsawa kauyen Adaysseh da ke arewa maso gabashin kasar.


Sojojin Lebanon sun kuma tabbatar da cewa sojojin na Isra'ila sun "kutsa kan Blue Line da kusan kimanin mita 400 zuwa cikin kasar Lebanon" a yankuna biyu, "sannan suka janye ɗan lokaci kadan."


A sa'i daya kuma, kungiyar Hizbullah ta ce ta kai jerin hare-hare kan sojojin Isra'ila da ke kan iyaka da kasar Lebanon, inda suka kai hari kan wasu wurare daban-daban na soji guda uku da rokoki da kuma makaman atilare, inda suka kai farmaki kai tsaye.


A wani bangaren kuma, kungiyar Hizbullah ta ce ta kai hari da rokoki da manyan bindigogi a matsugunan Misgav Am.


Babban jami’in yada labarai na Kungiyar Hezbullah Mohammed Afif ya fada a ranar Laraba cewa, kungiyar Hizbullah tana da isassun mayaka da makamai da alburusai da za su iya korar dakarun gwamnatin daga kasar.


Isra'ila ta yi iƙirari a ranar Talata cewa ta fara "iyakantaccen hare-hare ta ƙasa" a kudancin Lebanon.


A ranar Laraba, kafofin yada labaran gwamnatin sun yarda cewa sojojin su sun shiga cikin wani lamari da ba a saba gani ba kuma mai matukar wahala," wanda ya hada da kwashe wadanda suka jikkata daga yankin kan iyaka ta hanyar amfani da akalla jirage masu saukar ungulu guda hudu.


Sojojin sun kuma amince cewa dakarunsu sun fada cikin wani harin kwantan bauna da kungiyar Hizbullah ta shirya. Sun kuma ce kungiyar ta Lebanon tana yunkurin kai hari ga tarin sojojin Isra'ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post