Kungiyar Hizbullah Ta Sake Kai Wani Sabon Hari Da Makami Mai Linzami Kan Yankunan Isra'ila

 


Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sake kai wani sabon hari da makami mai linzami kan sansanonin sojin Isra'ila da matsugunan da ke arewacin kasar Falasdinu.


A cewar rahoton na Al Jazeera a ranar Laraba, Hezbollah ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ta kai hari kan taron sojojin Isra'ila a sansanin Shomera da makamai masu linzami. Kungiyar ta tabbatar da cewa makaman masu linzamin sun dira inda aka Aika su.


Da karfe 7:20 na safe agogon kasar, ƙungiyar Hizbullah ta kuma kai hari kan sojojin Isra'ila a yankin Shtula da makami mai linzami na Burkan guda biyu. 'Yan mintuna kadan kafin hakan, kungiyar ta harba rokoki da makamai masu linzami kan wata babbar rundunar sojojin Isra'ila da aka jibge a matsugunin Misgav Am. Kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, an kai wadannan hare-hare ne domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da gwagwarmayar Palastinawa, da kuma kare kasar Labanon.


Kafofin yada labaran Isra'ila sun rawaito cewa an yi wa sojojin Isra'ila kwanton bauna a kudancin kasar Lebanon, lamarin da ya yi sanadin jikkatar wasu da dama. Mazauna Isra'ila da dama sun jikkata a yankunan arewacin da aka mamaye, kuma kungiyoyin agaji sun tura akalla jirage masu saukar ungulu hudu domin kwashe wadanda suka jikkata. An bayar da rahoton cewa wani helikwaftan sojojin Isra'ila ya sauka a asibitin Rambam da ke birnin Haifa.


Da sanyin safiyar yau ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai hare-hare a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon, da suka hada da garuruwan al-Khiam, Kfarkela, da kuma garuruwan Marjaayoun.


 Sojojin Isra'ila sun fara kai hare-hare a kudancin Lebanon fiye da mako guda da ya gabata, inda aka ci gaba da kai hare-hare ta sama a tsawon mako. A cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon, hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da kuma jikkata dubbai ya zuwa yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post