Iran Ta Tsawaita Soke Dukkan Zirga-zirgar Jiragen Sama A Fadin Kasar


 Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ya bayyana cewa, za a soke dukkan zirga-zirgar jiragen sama a fadin kasar har zuwa karfe biyar na safiyar Alhamis domin kiyaye lafiyar jiragen da kuma yanayin yankin.


Bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai kan gwamnatin Sahayoniyya a daren ranar Talata, an yi shirye-shiryen da suka dace don jagorantar jiragen zuwa hanyoyi masu aminci, in ji Jafar Yazarlou a ranar Laraba.


Ya kara da cewa ana ci gaba da tantance hadurran da ke tattare da sararin samaniyar kasar da ayyukan jirage.


Da yammacin jiya Talata, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) sun harba wasu gungun makamai masu linzami kan sansanonin sojojin Isra'ila da ke yankunan Falasdinawa da suka mamaye a matsayin ramuwar gayya kan kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kwamandan IRGC Abbas Nilforoushan."

Post a Comment

Previous Post Next Post