Ministan Harkokin Wajen Iran: Ana Sa Ran Samun Kwanciyar Hankali A Yankin Nan Da Kwanaki Masu Zuwa

 


Kamar yadda rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana, idan har Gwamnatin Sahyoniya ko magoya bayanta suka dauki wani sabon mataki za su fuskanci martani mai tsanani daga Iran. Nayi Wannan gargaɗin tun a daren jiya, duka a cikin tattaunawa ta waya da kuma bayanan hukuma ga dukkan bangarorin, Araghchi ya fada a cikin wata hira ta gidan talabijin a ranar Laraba, yana tsokaci kan harin makami mai linzami da Iran ta kai kan gwamnatin Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila.


Da farko dai, musayar saƙonni ba yana nufin haɗin kai ba ne; na biyu, babu wata musayar sakwanni kafin harin, in ji shi.


Ya zama dole a gargadi dukkan bangarorin, ciki har da Amurka, bayan harin, wanda an riga anyi, in ji shi.


Wannan gargadin an riga an bayyana qarara ga ofishin jakadancin Switzerland da ke Tehran a daren jiya don isar da shi ga Amurkawa, in ji shi.


Sakon dai ya fi mayar da hankali ne kan cewa matakin tsaron da Iran din ta dauka ya dogara ne kan sashi na 51 na Yarjejeniya Ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma hakkinmu ne na kare hakkin mu.


Har ila yau babban hafsan hafsoshin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya bayyana a fili cewa idan har gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta mayar da martani to Iran za ta mayar da martani mai tsauri kuma za ta kai hari kan ababen more rayuwa na tattalin arziki.


A daren jiya, mun kai hari kan wuraren sojoji da na tsaro ne kawai, in ji shi.


Iran ta mayar da martani ga Isra'ila a yayin da dakarun IRGC suka harba makami mai linzami kan yankunan Falasdinawa (Hukumar Isra'ila) da ta mamaye a yammacin ranar Talata.


Dakarun tsaron kasar Iran IRGC sun bayyana cewa, sun fara kai wa wasu muhimman wurare na soji hari da makamai masu linzami.

Post a Comment

Previous Post Next Post