Kafofin yada labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, an samu tashin bama-bamai masu yawa a wasu sansanonin soji na gwamnatin, sakamakon harin makami mai linzami na Iran.
A cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu 'Sama', Kakakin rundunar yahudawan sahyoniya ya sanar da cewa, makamai masu linzami na Iran kai tsaye sun afkawa tsakiya da kudancin yankunan da aka mamaye.
A cewar wannan rahoto, sansanonin soji na gwamnatin sahyoniyawan sun fuskanci fashe-fashe a jere da munanan hare-hare sakamakon tasirin makamai masu linzami na Iran.
