Rundunar Al-Qassam ta kungiyar Hamas ta gudanar da wani harin roka mai karfi kan sansanonin abokan gaba na 'yan Sahayoniya a ranar farko da aka yi tunawa da Ambaliyar Al-Aqsa.
A cewar hukumar labarai ta Samaa, 'yan tawagar Al-Qassam sun yi amfani da bama-bamai na Rajum masu cin milimita 114 a kan sansanonin soja na Sufa da ke gabashin tashar Rafah.
A cikin sakon da suka fitar, rundunar Al-Qassam ta bayyana cewa 'yan tawagar su sun kawar da shinge da aka gina a kan iyaka a ranar 7 ga Oktoba, 2023, sun kama sansanonin sojan Isra'ila da ke kusa da yankin Gaza, sun kashe wasu daga cikin sojoji da mazauna a yankin, sannan sun kama wasu daga cikin su.
Bayan shekara guda da kashe-kashen da ke faruwa a Gaza, Isra'ila ba ta cimma burinta guda biyu ba, wato rushewar Hamas da ƙwato 'yan Isra'ila da aka kama.
Tun farkon yakin da ke faruwa a Gaza, an kashe kusan mutane 42,000 na Falasdinawa, mafi yawan su mata da yara.
