A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Hezbollah ta Lebanon ta sanar da cewa, a matsayin goyon baya ga Gaza da Gwagwarmayar Falasdinawa, da kuma a matsayin martani ga hare-haren da gwamnatin Sahayoniya ke yi, ta kai harin roka kan sansanonin Sojin Sahyoniyawa na Nimra, da ke yammacin Tiberias.
Hakanan, Hezbollah ta kai hari kan Matsugunan Karmiel na Sahayoniya da roka a karfe 6:55 na safiyar yau.
A wani lamari mai alaka, rundunar Al-Qassam ta kungiyar Hamas ta kaddamar da wani harin roka mai karfi kan sansanonin Isra'ila a ranar farko da aka yi tunawa da Ambaliyar Al-Aqsa.
Tare da bama-bamai na Rajum masu cin milimita 114, 'yan tawagar Al-Qassam sun kai hari kan sansanonin sojan Sufa da ke gabashin tashar Rafah, kamar yadda hukumar labarai ta Samaa ta ruwaito a farkon ranar Litinin.
