A cikin rahoton da The Guardian ta fitar, an bayyana cewa dabarun sojan Isra'ila sun gaza, musamman bayan yakin da suka yi da Lebanon da kuma martanin harin makamai masu linzami na Iran a makon da ya gabata. Wannan ya haifar da asarar rayuka a bangaren sojojin Sahayoniya, kuma hakan yasa ake ganin dabarun yakin Isra'ila sun fara raguwa.
Masana sun yi gargadin cewa, bayan hare-haren da Iran ta kai kan sansanonin sojojin Isra'ila, tare da asarar rayukan da suka samu a yakin Lebanon, dabarun yakin Isra'ila basu da tasiri. A ranar Litinin, jaridar The Guardian ta yi karin haske kan yadda tsarin sojan ya nuna rauni.
Jaridar ta ce: "Harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan Isra'ila ya nuna cewa sun yi tasiri matuka, ba kamar yadda shugabannin Isra'ila suka fara faɗa ba da farko, a maimakon haka, ya nuna cewa harin bawai kawai ya rikita makaman kariya na Isra'ila ba, har ma Iran ta iya kai hari mai inganci kan wuraren data nufa, musamman sansanonin soja," in ji jaridar Biritaniya.
Bayan shekara guda da fara wannan yaƙi mai fagage da yawa, wanda ya haɗa kasashe kamar Iran, Lebanon, Gaza, Yemen, Siriya da Iraq, ƙarfin sojan Isra'ila raguwa kawai yake yi, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Masana sun kuma yi gargadin cewa yaki mai nisa tsakanin Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na iya rikidewa zuwa irin yakin kai-da-kawo, duk da cewa Tel Aviv ta bayyana shirin mayar da martani cikin tsanaki.
A makon da ya gabata, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta kai harin martani kan Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami, a matsayin ramuwar gayya ga kashe-kashen da Isra'ila ta yi da laifukan da suka aikata a Falasdinu da Lebanon.
