A wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, a bikin tunawa da ranar Harin Ambaliyar Al-aqsa a ranar 7 ga Oktoba, Hezbollah ta yaba da jaruntakar da al’ummar Falasdinu suka nuna.
Duk da zalunci da tashin hankali da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi, wanda ya haifar da shahadar dubban Falasɗinawa da kuma lalata yankin Gaza, wannan tsarin na mulkin zalunci ya tabbatar da cewa ba zai iya tsayuwa ba tare da goyon bayan Amurka ba.
A wani ci gaba, ofishin jakadancin Iran a Lebanon ya bayyana cewa kasashen yankin ne za su yanke hukunci a kan yaƙin da ke faruwa a cikin yankin.
Yanzu Shekara guda ta wuce tun bayan Harin Ambaliyar Al-Aqsa, yayin da gwamnatin Sahayoniya ke ci gaba da aikata munanan laifuka a Gaza da Lebanon.
A ranar 7 ga Oktoba, 2023, kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta kai wani mummunan hari, wanda aka yi wa suna da Guguwa/Ambaliyar Al-Aqsa, kan gwamnatin mamaya.
Yankin Gaza ya ga ɗaya daga cikin mafi girman kisan kare dangi a tarihin dan Adam, wanda ya samar da kimanin Shahidai 42,000 da kuma fiye da Mutane 96,800 da suka samu raunika tun bayan barkewar yaƙin a cikin yankin.
