Hezbollah Ta Kai Hari Sansanin Sojan Isra’ila Kusa da Tel Aviv

 


Kungiyar gwagwarmayar Hezbollah ta Lebanon ta kai wani gagarumin hari kan sansanin sojan Isra’ila da ke wajen Tel Aviv, kusa da hedkwatar hukumar leken asiri ta Mossad. Wannan harin na rokoki ya kasance wani ɓangare na jerin hare-hare da Hezbollah ke gudanarwa karkashin shirin Khaybar Operations.


A cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, Hezbollah ta bayyana cewa sun kai harin ne kan sansanin Glilot, wanda ke dauke da rundunar 8200, wacce ita ce rundunar leken asiri mafi girma a sojojin Isra'ila, da ke da dubban sojoji.


A cikin wannan harin, Hezbollah ta kuma kai hari kan sansanin Nimra, wanda ke daya daga cikin manyan sansanonin sojojin Isra'ila a arewacin yankin Falasdinu da aka mamaye. Haka kuma, an kai hari kan wasu wuraren tattara motocin soja da dakarun makiya a kusa da Jal al-Alam. 


Kungiyar ta ci gaba da kai hare-hare kan wasu garuruwan Yahudawa da aka kafa ba bisa ka’ida ba, ciki har da Karmiel, Kfar Fradim, da Beit Hillel, tare da kai farmaki kan dakarun makiya a wurare da dama a kudancin Lebanon, ciki har da Rmeish da Blida.


Hezbollah ta bayyana cewa hare-haren sun kasance martani ne ga yakin kisan kiyashi da Isra'ila ke yi a Gaza, da kuma wani mataki na ramuwar gayya ga kisan dubban mutanen Lebanon da Isra'ila ta yi a cikin wannan rikicin.


A karshe, kungiyar ta sake jaddada aniyarta ta kare kasarta da mutanen da ake zalunta, tana mai cewa: "Juriya na nan daram, a shirye muke mu kare mutuncinmu da kasarmu. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen dakile makiya daga zalunci da girman kan su."

Post a Comment

Previous Post Next Post