Kwamandojin Iran Sun sha Alwashin Ɗaukar Fansa kan Kisan Haniyeh

 


Manyan hafsoshin sojin kasar Iran sun lashi takobin daukar fansa kan kisan da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran.


Ayau Alhamis ne babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri da kwamandan sojojin kasar Iran Abdolrahim Mousavi suka mayar da martani kan shahadar Haniyeh a birnin Tehran a safiyar Laraba.


Dole ne a dauki matakai daban-daban kuma tabbas sahyoniyawan za su yi nadama, in ji Manjo Janar Bagheri.


 Muna nan akan yadda zamu dauki fansa, in ji shi, ya kara da cewa tabbas hakan zai faru.


 A wani martani makamancin haka, Manjo Janar Mousavi ya sha alwashin daukar fansa kan kisan da aka yi wa shugaban siyasar Hamas.


Har ila yau, kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya mayar da martani kan lamarin, yana mai cewa, ya zuwa yanzu dukkanin ayyukan gwamnatin yahudawan sahyoniya sun samu amsa mai kyau.


An shahadantar Haniyeh da daya daga cikin masu tsaronsa a gidansu da ke babban birnin kasar Iran a ranar Laraba.


Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar jana'izar Haniyeh a yau Alhamis. Za a yi jana'izar Haniyeh a kasar Qatar da ke gabar tekun Fasha bayan wata sallar jana'izar a ranar Juma'a.


Muna roqon Allah daya karɓi shahadarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post