Isra'ila ta Kashe 'Yan Jarida 2 a Zirin Gaza: Rahoto

 


Wani harin da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe 'yan jaridar Aljazeera guda biyu bayan da suka tarwatsa wata mota a yammacin birnin Gaza, kamar yadda kafar yada labarai ta Qatar ta sanar.


A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ofishin yada labarai na Doha ya ce an kashe dan jaridar Al Jazeerar bangaren Larabci Ismail al-Ghoul da mai daukar hotonsa Rami al-Rifi a harin da aka kai wa wata mota kusa da yankin Aidia, yammacin birnin Gaza. .”


Al Jazeera tace kisan ba hatsari ba ne, da gangan aka yi shi, kuma za su yi kokarin ganin an hukunta wadanda suka aikata hakan.


"Mun yi Allah wadai da kashe 'yan jaridar Falasdinawa, muna kuma dorawa Isra'ila alhakin wannan danyen aikin. Muna kira ga al'ummomin kasa da kasa da kungiyoyin yada labarai da su matsa wa Isra'ila lamba kan ta dakatar da waɗannan take hakkin da take yi," in ji ta.


A cewar ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza, sabbin kashe-kashen sun kawo adadin ‘yan jaridar Falasdinawa da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza zuwa 165 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da Isra’ila ta kaddamar yaƙin kisan kare dangin kan Falasdinawa da ta killace.

Post a Comment

Previous Post Next Post