Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya mika ta'aziyya ga al'ummar musulmi akan Shahadar Ismail Haniyyah da Jagora Mujahid Fouad Shukr, inda ya yi alkawarin daukar fansa kan haramtacciyar kasar Isra'ila.
A cikin bayanin Sayyed Abdulmalik ya tabbatar da cewa da yardar Allah tare da hadin kan 'yan uwanmu a cikin tafarkin jihadi da tsayin daka, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar fansa kan dukkan shahidai da kuma magance zaluncin da Palastinawa suke fuskanta.
Ya kuma jaddada cewa shigar makiya masu aikata laifuka wajen kai wa shahidin hari yana kara ruruta wutar rikici zuwa wani matsayi mai girma, kuma akwai mummunan sakamako ga makiya insha Allah.
Ya tabbatar da cewa laifin kaiwa mai girma Mujahid Isma'il Haniyyah hari zai kasance a matsayin wani babban abin karfafa gwiwa ga 'yan gwagwarmaya, da ibada a tafarkin Allah, da kuma azabtar da makiya masu laifi.
Jagoran ya bayyana cewa, ana fuskantar kisan kiyashi da Isra'ila suka yi wa al'ummar Palastinu a cikin watanni goma da suka gabata.
Sayyid Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa Gwagwarmayar Musulunci ta daga tutar jihadi tare da tsayawa tsayin daka a kan al'ummar Palastinu da ake zalunta har sai ta cimma gagarumar nasara.
