Dan jaridan Amurka: Dakatar da Shigar da Makamai Zuwa Isra'ila ne Kawai Zai Kawo Karshen Kisan Kiyashi

 


Hanya daya tilo da za a kawo karshen yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza ita ce Amurka ta dakatar da jigilar makaman da take yi wa gwamnatin kasar, in ji wani dan jarida, marubuci kuma mai fafutuka da ya lashe kyautar Pulitzer da ke Amurka.


A cikin wani sakon da ya wallafa a shafin shi na X, Chris Hedges ya ce akwai "hanya daya da za'a iya kawo karshen yakin kisan gillar da ya yi sanadin rayuka sama da 40,000"ba ta hanyar tattaunawa tsakanin kasashe biyu ba."


Ya kuma ce, "ayyukan Isra'ila, ciki har da kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh, ya nuna a fili cewa ba ta da sha'awar tsagaita wuta na din din din."


“Hanya daya tilo da za a dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa ita ce Amurka ta kawo karshen shigar da makamai da take yi wa Isra’ila. Kuma hanya daya tilo da hakan zai faru ita ce idan isassun Amurkawa sun bayyana karara cewa ba su da niyyar tallafawa duk wani tikitin takarar shugaban kasa ko kuma wata jam’iyyar siyasa da ke rura wutar wannan kisan kare dangi.”


Hedges, wanda ya yi aiki a matsayin wakilin kasashen waje na New York Times, Rediyon Jama'a na kasa da sauran fitattun kungiyoyin labarai na kusan shekaru ashirin, ya yi matukar suka ga hadin kan Amurka a yakin kisan kare dangi da Isra'ila ta yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.


A cewar sabon bayanan da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayar, adadin wadanda suka yi shahada a yakin kisan kare dangi ya haura 40,099 baya ga 92,610 da suka jikkata.


Yayin da kuma dubbai na ci gaba da makalewa a karkashin baraguzan ginin, da ake kyautata zaton sun mutu.

Post a Comment

Previous Post Next Post