Wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas ya ce gwamnatin sahyoniyawa ce take ta jan ƙafa a yakin zirin Gaza tare da jinkirta shirin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Husam Badran ya ce Isra'ila na jinkirta tsagaita bude wuta a rikicin Gaza, a cewar Sama news.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana kawo cikas ga shirin cimma matsaya a yankin, inda ya kara da cewa Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu suna kira da a kawo karshen yakin da kuma dakatar da kashe fararen hula a yankin.
Jami'in na Hamas ya kuma bayyana cewa, Amurka na ci gaba da yin rufa-rufa a kan irin ta'asar da gwamnatin sahyoniya ta yi.
Ya ce Falasdinawa na bin sharuddan da aka amince da su a tattaunawar da aka yi a ranar 2 ga watan Yuli, shawarar da Isra'ilawa suka gabatar kuma tana karkashin shirin Joe Biden da kuma kudurin kwamitin sulhu na MDD.
A ranar Alhamis din da ta gabata ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da wani sabon adadi, inda ta ce adadin wadanda suka mutu a yakin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza ya kai 40,005 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 92,401, yawancinsu mata da kananan yara.
