Tsohon ministan Isra'ila ya ce Gwamnatin Isra'ila tayi Matukar Kunyata a Gaza


 Shugaban jam'iyyar Isra'ila Beytenu Avigdor Liberman ya Tabbatar da cikakkiyar Wulakantuwa da Kunyatar da Gwamnatin Sahyoniya ta yi a Maimakon Nasara a Gaza.


Bayan watanni takwas na yaki, Isra'ila ta yi rashin nasara a arewa, ta samu wulakanci maimakon nasara, sannan ta yi rashin nasara a yakin da take yi da Hizbullah wadda ke yin duk abin da ta ga dama, kamfanin dillancin labaran IRNA ne ta ambato hakan daga kafafen yada labaran kasashen waje a yau Asabar


A yakin da aka fara a watan Oktoban shekarar 2023, Isra'ila ta kasa gamawa da Hamas, ta kuma kasa kwato mutanen ta daga Gaza, in ji Al Mayadeen a cewar Liberman.


A wani labarin kuma, madugun 'yan adawar Isra'ila Yair Lapid ya bayyana majalisar ministocin Benjamin Netanyahu a matsayin masu cin hanci da rashawa, yana mai cewa firaministan kasar ba zai iya inganta munanan yanayin siyasa a gwamnatin kasar ba.


Har ila yau, gidan rediyo da talabijin na gwamnatin kasar sun riga sun ba da rahoton cewa Benny Gantz, memba a majalisar ministocin yakin Isra'ila, zai yi murabus a ranar Asabar, wanda zai iya haifar da rushewar majalisar.


A halin yanzu, gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta bukaci Gantz da kada ya yi murabus a halin yanzu.


 Tun lokacin da aka fara yaki a Gaza, gwamnatin yahudawan sahyoniya ta Isra'ila ke kara nutsewa cikin rikicin cikin gida da waje.


Ta'addancinta bai kawo komai ba illa rusawa, kisan kiyashi, laifuka da yunwa a zirin Gaza.


 Tun farkon yakin, an kashe Falasdinawa sama da 36,000 galibi mata da kananan yara a zirin Gaza.


Muna Rokon Allah daya ƙara kunyatar dasu, ya kuma cigaba da ba 'yan gwagwarmayar Musulunci Nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post