Mummunan harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 274, yayin da wasu 698 suka samu raunuka, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassan duniya.
Harin wanda ya auku a ranar Asabar, an bayyana shi a matsayin daya daga cikin munanan laifukan da Isra'ila ta yi a cigaba da Kisan kiyashin da take yiwa Al'ummar Falasdinu. Hukumar Falasdinu ta yi kira da a gudanar da zaman gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin shawo kan lamarin.
Asibitoci a Gaza na kokawa kan kwararar wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin wadanda aka kashe, inda rahotanni ke nuni da cewa da dama daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali. Jami'an tsaron farar hula na ci gaba da neman wadanda suke raye a karkashin baraguzan ginin, yayin da ake ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankunan da ke kewayen.
Hare Haren sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila wanda suka fara ƙaddamarwa tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 37,084 tare da jikkata wasu 84,494, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.
Kasashen duniya dai sun yi tir da wannan harin, inda kasashe da kungiyoyi da dama ke yin kira da a gaggauta kawo karshen hare haren da kuma daukar nauyin masu hannu a ciki.
Kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ta Falasdinu ta soki matakin da sojojin Isra'ila suka dauka a matsayin gazawa bisa manyan tsare-tsare tare da zargin Amurka da hannu a laifukan yaki da ake tafkawa a Gaza.
Har yanzu dai lamarin na ci gaba da ruruwa, inda ake ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma kai hare-hare ta sama, lamarin da ya zama kalubale ga masu ba da agajin gaggawa wajen kaiwa ga mabukata. Al'ummar duniya na yin kira da a gaggauta tsagaita bude wuta tare da cimma matsaya kan rikicin.
