Dakarun Yaman sun Ƙaddamar da Farmakin soji Domin Tallafawa Falasdinu

 


A wani mataki na ba-zata, Dakarun Yaman sun kaddamar da wani farmakin soji domin nuna goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu, inda suka nufi wani jirgin ruwan yaki na Birtaniya da wasu jiragen ruwa guda biyu a tekun Bahar Maliya da Tekun Larabawa.


A cewar sanarwar da rundunar sojin Yaman ta fitar, an kai harin ne a matsayin martani ga kisan kiyashi da aka yi a sansanin Nuseirat da ke zirin Gaza. Dakarun makami mai linzami sun kai hari kan Jirgin Ruwan Yaƙin ‘Diamond’ na Burtaniya da makamai masu linzami da dama, inda Harin yaje inda aka Aika shi.


Bugu da kari, sojojin ruwa, da sojojin makami mai linzami, da Sojojin Jirage sama marasa matuƙa (Drone Air Force), sun kai farmakin hadin gwiwa guda biyu kan jiragen ruwa guda biyu na wasu kamfanoni da suka karya dokar hana shiga tashar jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye. Jiragen da aka bayyana sunayensu da "Norderney" da "MSC Tavvishi" harin ya same su ne kai tsaye, lamarin da ya haddasa gobara a kan daya daga cikinsu.


Dakarun kasar Yemen sun bayyana cewa, za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na addini, da'a, da kuma jin kai ga al'ummar Palastinu har sai an daina kai hare-hare a zirin Gaza.


Wannan farmakin dai ya nuna wani gagarumin ci gaba a goyon bayan da kasar Yamen ke baiwa Falasdinu, kuma ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post