Shin Isra'ila Zata Cigaba da Wanzuwa Kuwa Bayan Haramcin da Colombia ta yi na fitar da Kwal?

 


Isra'ila na ƙara fuskantar karin killacewar duniya yayin da Colombia ta sanar da dakatar da fitar da gawayi (Coal), inda ta zama kasa ta farko a yankin Latin Amurka da ta kakaba takunkumin kasuwanci kan Haramtacciyar Kasar Isra'ila saboda Kisan Kiyashin da take yi a Zirin Gaza.


A cewar IRNA inda ta nakalto daga Jaridar El Pais, Shugaba Gustavo Petro ya sanar da matakin ne a ranar Asabar ɗin da ta wuce, Colombia ta ɗauki wannan matakin ne saboda kisan kiyashin da HKI take yiwa Falasdinawa har yanzu.


Petro ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na X ranar Asabar cewa, "Za mu dakatar da fitar da gawayi (Coal) zuwa Isra'ila har sai an daina kisan kare dangi," ya kara da cewa an shirya wani daftarin doka da ta bayyana karara cewa fitar da gawayin (Coal) zai dawo ne kawai idan gwamnatin ta bi umarnin Kotun duniya kan Gaza. 


Shin wane irin tasiri wannan mataki zaya yi kan gwamnatin Sahayoniya da tattalin arzikinta?


Kolombiya ita ce ta fi kowacce Ƙasa fitar da gawayi (Coal) zuwa Isra'ila, inda gwamnatin ke cin kashi 90% na kwal da ake shigo mata da shi, wanda kuma kaso 61.5% na Wutar lantarkin su yana samuwa ne ta hanyar wannan Kwal ɗin.


 A cewar wasu bayanai na hukuma da wani kamfanin dillancin labarai ya ambato, Colombia ta ba wa gwamnatin sahyoniyar kwal na kimanin dalar Amurka miliyan 450 a shekarar 2023 amma kuma adadin ya ragu matuka a watanni hudun farko na shekarar 2024.


Shin gwamnatin sahyoniyawan da ke nutsewa a zirin Gaza za su fita daga wannan sabon rikicin?


Majiyoyin yada labarai sun ce, la'akari da kasar Colombia a matsayin kasar da ta fi samar da albarkatun makamashi (Fossil Fuels) a Isra'ila, wannan mataki na iya shafar huldar kasuwanci tsakanin Bogota da Tel Aviv.


Wannan mataki, wanda kuma ministocin harkokin waje, na kudi da makamashi na Colombia suke goya ma baya, za'a aiwatar da shi ne bayan sanya hannun shugaba Petro, wanda a halin yanzu yake nahiyar Turai don halartar wani taro kan Ukraine.


 A watan da ya gabata, Petro ya sanar da yanke huldar jakadanci da Isra'ila. Sai dai matakin na baya-bayan nan dai wani babban koma-baya ne ga gwamnatin Sahayoniya domin ta dogara kacokan kan fitar da gawayi daga kasashen Latin Amurka.


Tun farkon yakin kisan kare dangi da Isra'ila ta yi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, Petro ya sha sukar Isra'ila tare da yin kira ga sauran kasashen Latin Amurka da su tafi tare da Colombia wajen yin Allah wadai da Isra'ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post