Al'ummar Indonesia Sun yi tir da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza

 


Al'ummar Indonesiya sun gudanar da wani gagarumin gangami a Jakarta babban birnin kasar domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da kuma yin kira da a kawo karshen laifukan da yahudawan sahyuniya suke yi a zirin Gaza.


A cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA, Jama'a sun gudanar da jerin gwano a yankuna daban-daban na birnin Jakarta a yammacin jiya Lahadi inda suka bukaci kawo karshen yakin Gaza da kuma karin taimako daga gwamnatinsu ga al'ummar Palasdinu.


 Rahoton ya ce, jama'a daga sassa daban-daban sun hallara tare da nuna kakkausar suka dangane da kisan gillar da 'yan mamaya ke yi wa Falasdinawa.


Wasu 'yan kasar Indonesiya sun kuma bukaci kasarsu ta taimaka wa al'ummar Palasdinu ta hanyar soji, suna mai bayyana Isra'ila a matsayin "tabbatacciyar 'yar ta'adda".


 Sun yi Allah wadai da gwamnatin sahyoniyawan da take kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba da kuma luguden wuta a Gaza wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 37,000 galibi mata da kananan yara.


Al'ummar Indonesiya sun gudanar da taruka da dama na nuna goyon baya ga Falasdinawa tun bayan da gwamnatin sahyoniyawan ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a watan Oktoban bara.

Post a Comment

Previous Post Next Post