Rundunar sojan Amurka ta CENTCOM ta tabbatar a jiya Lahadi cewa dakarun kasar Yemen sun harba makamai masu linzami da suka lalata wasu jiragen ruwa biyu na kasuwanci a mashigin tekun Aden cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A cewar CENTCOM, dakarun Houthi sun harba makami mai linzami guda biyu (ASBM) daga kasar Yemen, inda suka afkawa jirgin ruwan kwantena M/V Tavvishi mai tutar Laberiya da kuma na Antigua da Barbuda na daukar kaya M/V Norderney. Dukkanin jiragen biyu sun ba da rahoton lalacewa amma sun ci gaba da aiki. Ba a samu rahoton jikkata ba
Dakarun na CENTCOM sun yi nasarar tarewa da kuma lalata wasu karin makamai masu linzami na Houthi, ciki har da makami mai linzami na yaƙar jiragen ruwa (ASCM) daya hari M/V Norderney, da kuma wani jirgin sama mara matuki (UAS) da makami mai linzami na kasa (LACM) a yankunan da Houthi ke iko na kasar Yemen.
Birgediya Janar Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman ya tabbatar da alhakin kai hare-haren, yana mai bayyana cewa Dakarun Yaman sun kai hari kan jirgin ruwan Birtaniyya na Diamond da ke tekun Bahar Maliya da kuma wasu Jiragen ruwa biyu na kasuwanci, domin nuna goyon bayan Falasɗinawa da kuma nuna adawa da ci gaba da cin zarafi kan zirin Gaza.
