A wani muhimmin mataki da MDD ta dauka, ta saka Isra'ila cikin Baƙin Shafin ta na masu take hakkin yara, saboda irin abubuwan da ba a taba ganin irinsu ba na munanan cin zarafin yara a yankunan da ta mamaye.
A cewar wani rahoto da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi yace "cin zarafin kananun yara ya karu da kashi 21% a shekarar 2023, inda aka samu karuwar mace-mace da jikkata da kashi 35% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Rahoton, wanda aka shirya za a buga shi a hukumance ranar Alhamis, ya tabbatar da cin zarafi sama da 8,000 kan yara 4,360 a Isra'ila, Gaza, da Yammacin Kogin Jordan.
Rahoton ya yi Allah wadai da ayyukan Isra'ila a zirin Gaza, inda take hakkin yara ya karu da kashi 155%. Ana zargin sojojin yahudawan sahyoniya da katse hanyoyin kai agaji a Gaza, gabar yammacin kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus. Guterres ya bayyana kaɗuwarsa dangane da karuwar kashewa da kuma Jikkata kananan yara da sojojin Isra'ila keyi.
Shigar da Isra'ila cikin Baƙin Shafin ya biyo bayan yaƙin da aka shafe watanni takwas ana gwabzawa a Gaza, wanda ya lakume rayukan yara sama da 14,000 da fararen hula 37,000. Matakin dai ya janyo cece-ku-ce daga gwamnatin Isra'ila, inda wakilinta a MDD ya yi tir da matakin da cewa abin kunya ne.
Wannan gagarumin ci gaba ne, wanda ya ɗaura alhakin abubuwan dake faruwa da kananan yaran na Falasɗinawa kan Isra'ila. An yi kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai don tabbatar da kare yara a fadace-fadace.
