Kungiyar Gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hari kan Yankunan Falasdinu da Aka Mamaye da ke Arewaci, da Aƙalla Makamai Masu Linzami Guda 100.
Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton cewa, a karon farko an fara jin karar sautin "Sirens" tun bayan barkewar yaki a ranar 7 ga watan Oktoba a birnin Tiberias da ke yammacin tekun Galilee.
Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami kan yankunan da aka mamaye, wanda shi ne harin makami mai linzami mafi girma ta fuskar adadi da nau'in makaman da aka harba.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce an cigaba da jin karar fashewar abubuwa da kuma "Sirens" ba tare da ƙaƙƙautawa ba a yankin Saman Galilee da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye. Har ila yau kungiyar ta Hizbullah ta kai hari kan kamfanin makamai na Rafael na gwamnatin kasar.
Kafofin yada labaran sun kuma bayar da rahoton katsewar wutar lantarki a yankuna daban-daban na birnin Safed da ke yankin Arewacin Falasɗinu da Isra'ila ta mamaye bayan harin makami mai linzami da kungiyar Hizbullah ta kai.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu, Sama, ta ba da rahoton wani gagarumin hari da aka kai kan sansanonin sojan Isra'ila na Miron, wanda ke arewacin Falasdinu da aka mamaye, wanda aka fi sani da tsaunin Miron ko Jabal al-Jarmaq. A cewar rahoton, adadi mai yawa na makamai masu linzami sun afkawa sansanin da kewaye.
Har yanzu babu wani rahoto kan irin hasarar da gwamnatin Sahayoniya ta yi bayan wadannan hare-hare.
