Amurka da Birtaniya sun kai hare-hare da dama ta sama a cikin daren jiya Laraba a yammacin Yaman kan goyon bayan da take baiwa Falasdinawa da ake zalunta a zirin Gaza.
Tashar talabijin ta Al Masirah ta kasar Yemen ta ce mutane biyar ne suka jikkata, wanda lamarin ɗaya daga cikinsu yayi muni sosai, bayan da jiragen yakin Amurka da Birtaniya suka kai hari a lardin Rima.
A cewar wannan rahoto, an hari ginin gwamnati ne a yankin Al-Jebin na lardin Rima inda aka kai masa hari har sau biyu.
A 'yan sa'o'i kadan da suka gabata, kafofin yada labaran kasar Yemen sun ba da rahotan an kai irin wadannan hare-hare kan birnin al-Tahita da kuma yankin Al-Jabanah da ke lardin Hudaidah, wanda dukkan su suke a yammacin kasar Yemen.
Kawo yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna cewa an samu hasarar rayuka ko barna a harin na farko da aka kai a yammacin Laraba.
Yankunan Yemen daban-daban, musamman Hudaida, sun fuskanci hare-haren wuce gona da iri na Amurka da Birtaniya a cikin watannin da suka gabata.
Kasashen yammacin biyu na ci gaba da kai farmakin hadin gwiwa a kan kasar Yamen da nufin matsin lamba kan ta dakatar da shingen da sojojin ruwan ta suka yi wa gwamnatin sahyoniyawan. Hare-haren ba wai keta hurumin kasar Yemen ne kadai ba har ma sun sabawa kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ba da damar daukar matakan kare hanyar jiragen ruwa, ba tare da hkai wa wata kasa hari ba.
Sai dai sojojin kasar Yemen sun yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila ko Jiragen dake da alaƙa da Isra'ila a tekun Bahar Rum har sai lokacin da gwamnatin sahyoniyawan ta dakatar da yakin da take yi na kisan kare dangi a Gaza, tare da kawo karshen killace yankin Falasdinu. Har ila yau ta kaddamar da hare-hare kan jiragen ruwa na Amurka da na Biritaniya a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da kasashen biyu ke kaiwa kasar Yemen.
