Kungiyar Ilimi ta Italiya ta yi Allah-wadai da Ayyukan Isra'ila a Gaza

 


A ci gaba da nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu, jami'o'i da malaman jami'o'in Italiya na kara nisantar da kansu daga Isra'ila a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.


Jami'ar Palermo ta dauki nauyin jagoranci, inda ta dakatar da duk wata alaka ta ilimi da cibiyoyin Isra'ila tare da soke shirin musayar dalibai da Tel Aviv. Jami'ar Turin kuma ta ki shiga wani shiri na hadin gwiwa a fannin kimiyya da Isra'ila, saboda mummunan ayyukan da takeyi a Gaza.


Kungiyar ma'aikatan jami'o'i da daliban jami'o'i da ke ci gaba da yin kira da a kaurace wa Isra'ila, suna masu yin Allah wadai da matakin da ta dauka "na cigaba da kisan kare dangi" da "rashin dan Adamtaka". Zanga-zangar ta kunno kai a manyan cibiyoyin jami'o'i, inda ake neman kawo karshen hadin gwiwa da Isra'ila tare da dakatar da fitar da makamai zuwa Tel Aviv.


A cikin gagarumin nunin goyon baya, sama da malaman jami'o'in Italiya 2,000 sun rattaba hannu kan wata budaddiyar wasika a cikin watan Afrilu, suna kira ga cibiyoyin Italiya da su kiyaye wajibcinsu na hana hada hannu a ayyukan kisan kiyashi, kamar yadda yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ta 1948 ta ayyana.


Wannan mataki na nuna adawa daga ƙungiyar ilimi ta Italiya na nuna babban sauyi da aka samu na ra'ayoyin Jama'a a duk faɗin Turai, tare da yin Allah wadai da ayyukan Isra'ila a yankunan da ta mamaye. 

Post a Comment

Previous Post Next Post