Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Yahya Saree ya sanar a jiya Juma'a cewa an kai hari kan wasu jiragen ruwa guda biyu a tekun Bahar Rum.
Saree ya sanar a cikin wata sanarwa cewa, a hare-haren hadin gwiwa guda biyu da aka kai a tekun Bahar Maliya, sojojin ruwan Yaman da dakarun makami mai linzami sun kai hari kan jiragen ruwan Elbella da AAL GENOA na wasu kamfanonin da suka keta dokar hana shiga tashar jiragen ruwan Falasdinu da aka mamaye.
Saree ya ce "Hare Haren da sojojin mu ke yi, ana yin sune domin nuna goyon bayan al'ummar Falasɗinu da kuma mayar da martani ga laifukan da gwamnatin Sahayoniya ke yi kan 'yan gudun hijira a Rafah da kuma hare-haren da Amurka da Birtaniya ke kaiwa Yemen."
Ya kuma jaddada cewa, za a ci gaba da gudanar da hare haren sojin har sai an kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Gaza tare da kawo karshen killace wannan yanki.
Saree ya sanar da cewa harin da aka kai kan wadannan jiragen ruwa guda biyu da jirage marasa matuka da makamai masu linzami anyi nasarar su.
