Dakarun Islama na Iraki Sun Tabbatar da Farmakin Hadin Gwiwa da Ƙasar Yemen


 A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki ta tabbatar a yau Alhamis cewa ta gudanar da wani farmakin soji na hadin gwiwa tare da kasar Yamen kan gwamnatin sahyoniyawa.


A cewar Aljazeera, Kungiyar gwagwarmayar muslunci ta kqasar Iraki ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, ta gudanar da hare-haren soji na hadin gwiwa guda biyu tare da dakarun kasar Yaman kan gwamnatin sahyoniyawa.


A cikin wannan sanarwa, an bayyana cewa an gudanar da wadannan hare haren guda biyu ta hanyar amfani da jirage marasa matuka kuma a tashar jiragen ruwa na Haifa.


Muna roqon Allah daya cigaba da taimakon 'Yan Gwagwarmayar Musulunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post