Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai wani hari kan wani gini da ke arewacin yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye inda da dama daga cikin sojojin HKI suka taru, kamar yadda Kafofin yada labarai na cikin gida suka ruwaito.
Al Ahd News ta naƙalto wata sanarwa daga Hezbollah a yau Asabar cewa an kai harin ne kaitsaye akan ginin.
Ta ce harin an kai shine domin nuna goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa a zirin Gaza da kuma daukar fansa kan hare-haren da yahudawan sahyuniya suka kai kan kauyukan kudancin kasar Labanon.
Akwai kuma rahotannin cewa wani jirgin yaki mara matuki na yahudawan sahyoniya ya kai hari kan wata mota a yankin Khara da ke gundumar Beqaa ta Yamma a kasar Lebanon.
Sojojin yahudawan sahyoniya sun yi ikirarin cewa an kashe Ayman Ghatma, wani jigo a kungiyar al-Jama’a al-Islamiyya a harin.
Har yanzu Al-Jama’a al-Islamiyya ba ta tabbatar da kashe shi ba”.
