Kasar Cuba Tabi Sahun Afirka ta Kudu Wajen Tuhumar Isra'ila

 


Kasar Cuba ta bayyana matakinta na shiga cikin karar da Afrika ta Kudu ta shigar a watan Nuwamba a gaban kotun kasa da kasa (ICJ) kan kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a zirin Gaza.


Gidan rediyon Havana ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin wajen Cuba ta sanar da matakin da ta dauka a safiyar yau Asabar, inda ta ce an dauki matakin ne daidai da kokarin da kasashen duniya ke yi na kawo karshen kisan kiyashi a Gaza.


Gwamnatin Cuba, a bisa doka ta 63 na yarjejeniyar kisan kare dangi ta ICJ, tana amfani da ‘yancinta a matsayinta na kasa ta uku na shiga shari’ar kin jinin HKI a kotun duniya.


 Cuba ta bayyana Isra'ila a matsayin 'yar mamaya da ta yi watsi da yarjejeniyar ta hudu ta Geneva, wadda ta ce "Za'a kare fararen hula a wuraren da ake fama da rikici da kuma yankunan da aka mamaye."


A yau, al'ummar duniya ba sa yarda da kisan kare dangi, wariyar launin fata, tilastawa 'yan gudun hijira da kuma azabtar da jama'a, in ji Havana.


 A watan Nuwamba ne Afirka ta Kudu ta shigar da kara gaban kotun ICJ domin ta dorawa gwamnatin Sahayoniya alhakin laifukan yaki a Gaza.


 Hukuncin farko na ICJ a watan Janairun 2024, ya umarci gwamnatin Isra'ila da kada ta dauki matakin kisan kare dangi a Gaza.


A wani labarin kuma, shugaban ICJ, Alkali Nawaf Salam, ya ce Afirka ta Kudu ta kara da karar da ta shigar kan Isra'ila tare da zargin gwamnatin kasar da aikata kisan kiyashi a Gaza.


 Har ila yau, mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, Karim Khan, ya yi kira da a kamo firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu saboda laifukan yaki da cin zarafin bil'adama.


 Idan alkalan kotun ta ICC suka amince da kiran, ya wajaba akan kasashe 124 na kotun kasa da kasa su kama shi.


 Tun lokacin da Isra'ila ta fara yakin Gaza, an kashe Falasdinawa sama da 37,000 galibi mata da kananan yara a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post