UKMTO Tace ta Samu Rahoton Harin da Aka Kai kan Wani Jirgin Ruwa a Kusa da Kasar Yemen

 


Kungiyar hada-hadar kasuwanci ta ruwa ta Burtaniya (UKMTO) ta sanar da cewa ta samu rahoton wani lamari da ya faru da wani jirgin ruwan kasuwanci a gabashin Aden na kasar Yemen.


 Kamfanin ya bayyana hakan ne a safiyar yau Asabar a kan X, wanda a baya ake kiranta da Twitter.


 Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma'a a wani guri mai nisan mil na ruwa 126 daga gabashin Aden.


“Kyaftin ɗin Jirgin ne ya ba da rahoton fashewar, inda yace sunji ƙarar fashewar abubuwa a kusa da jirgin. An ba da rahoton cewa ma'aikatan jirgin suna cikin koshin lafiya kuma jirgin na tafiya zuwa tashar jiragen ruwa na gaba", in ji UKMTO a shafinsu na x, sun ƙara da cewa an fara gudanar da bincike. 


Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga kasar Yemen dangane da lamarin.


Tun a tsakiyar watan Nuwamba 2023, Yemen ta fara kai hare-hare kan jiragen ruwan HKI ko Jiragen ruwan da suka nufi tashar jiragen ruwan yankunan Falasdinawa da ta mamaye a matsayin martani ga yakin da gwamnatin HKI ke yi a Gaza.


 Kasar Yemen ta ce tana kai hare-haren nata ne da nufin matsa wa gwamnatin HKI lamba kan ta dakatar da hare-haren da sojojinta ke kai wa a Gaza da kuma janye shingen da ta yi wa yankin Falasdinu inda kusan daukacin al'ummar kasar ke fuskantar karancin kayan masarufi.


Kasar Yemen na ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila a kan teku duk da hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen tun a tsakiyar watan Janairu. 


Kasar ta Larabawa ta ce hare-haren da ake kai mata ta sama ana yin shine da nufin baiwa gwamnatin HKI karin goyon baya ne kawai.    

Post a Comment

Previous Post Next Post