'Yan Gwagwarmayar Kasar Iraqi sun kai hari da jiragen yaki mara matuki a kudancin Palasdinu da aka mamaye


Kafafen yada labaran kasar Iraki sun sanar da cewa, kungiyar Gwagwarmayar ta kasar Iraki ta kaddamar da wani hari da jiragen yaki marasa matuka a kudancin Palasdinu da aka mamaye.


Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Iraki sun sanar cewa sun kai hari kan wani muhimmin wuri a yankin Eilat da aka mamaye tare da jirage marasa matuka guda biyu a wani yunkuri na tallafawa mutanen Gaza da kuma mayar da martani ga laifukan gwamnatin sahyoniyawan. Kamfanin dillancin labaran Sama na Falasdinu ne suka ruwaito hakan.


Kungiyar ta 'yan gwagwarmayan ta jaddada ci gaba da kai hare-hare kan yahudawan sahyoniya, inda ta kara da cewa, an yi amfani da jiragen Al-Arfad a karon farko wajen kai harin.


Kungiyar Gwagwarmayar ta Ƙasar Irakin ta gargadi yankunan da aka mamaye a baya bayan nan cewa za ta kara kaimi wajen yaki da gwamnatin Haramtacciyar Kasar ta Isra'ila idan har gwamnatin ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.


 Tun lokacin da aka fara yakin a Gaza a watan Oktoban 2023, kusan Falasdinawa 35,000 wanda mafi yawan su yara da mata ne suka rasa rayukansu.


Kungiyoyin 'yan Gwagwarmayar yankin sun kai hare-hare kan wuraren Isra'ilan tun bayan da gwamnatin Haramtacciyar kasar ta kaddamar da yakin Gaza a farkon watan Oktoba.


 Kungiyoyin sun yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa.


Allah ya qara taimakon 'Yan Gwagwarmayar Musulunci a duk inda suke.

Post a Comment

Previous Post Next Post