Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta ce ta kaddamar da hare-hare iri-iri kan yankunan da Isra'ila ta mamaye a arewacin kasar Falasdinu.
Tashar talabijin ta Al-Manar ta bayar da rahoton a yau Talata cewa kungiyar Hizbullah ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama a yankin Metula da ke yankunan da ta mamaye.
Tun da farko dai, Kungiyar gwagwarmayar ta lalata wasu tankokin yaki na sojojin gwamnatin sahyoniyawan tare da kashe da kuma raunata sojojin yahudawan sahyoniya da dama a wasu hare-haren jiragen sama marasa matuka da na rokoki a arewacin Palastinu da zirin Gaza ta mamaye.
.jpeg)